RUNDUNAR SOJOJI SUN KAI ZIYARA ASIBITI DA GIDAJEN WADANDA HATSARI YA RUTSA DA SU A DAMATURU DON YI MUSU GAISUWA - Arewa24blogs

Breaking

Post Top Ad

Post Top Ad

Monday 11 November 2019

RUNDUNAR SOJOJI SUN KAI ZIYARA ASIBITI DA GIDAJEN WADANDA HATSARI YA RUTSA DA SU A DAMATURU DON YI MUSU GAISUWA

A madadin rundunar Sojoji Kwamandan ruko na sashe na biyu karkashin jagorancin OPERATION LAFIYA DOLE, Brigadier Janar Ibrahim Sallau Ali, na mika gaisuwa da alhini ga Iyaye da dangin wadanda hatsarin Mota ya rutsa da su tare da Motar zagayen Sojoji garin Damaturu,a ranar Asabar 9 ga watan Nuwambar wannan Shekarar ta 2019 da muke a ciki.
Rundunar Sojojin sun kadu matuka tare da shiga damuwa kan hatsarin musamman ganin an yi rashin Ran matshiyar Budurwa kuma daluba a makarantar kimiya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake babban birni jihar Yobe Damaturu.
Janar Sallahu, ya bayyana haka ne a wata zungureriyar takarda daya rabewa manema Labaru.

See more https://www.bestblog.com.ng/2020/01/jamb.html
Ya ce, Rundunar sashe na biyu suna masu amfani da wannan damar don nuna rashin jin dadin su tare da mika gaisuwa ga Iyaye da dangin wadanda hatsarin ya rutsa da su tare da Adduar Allah ya tashi kafadar wadanda suke kwance a gadon Asibiti.
Kazalika takardar ta kara da cewar tun tuni hukumr Sojojinga ta aike da mutanen ta zuwa gidan wadanda suka rasa ran nasu don jajantawa wadanda abun ya shafa, a lokaci guda kuma ta kafa Kwamiti na musamman don jin korafe korafe da jin koken dalilin faruwar hatsarin da bashi da dadin ji.


No comments:

Post a Comment

Post Top Ad