Buhari Ya Aika Da Tirela Makare Da Kayan Gini Zuwa Garin Daura - Arewa24blogs

Breaking

Post Top Ad

Post Top Ad

Tuesday 3 September 2019

Buhari Ya Aika Da Tirela Makare Da Kayan Gini Zuwa Garin Daura

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya musanta zargin da ake yi masa a kan cewa ya juya wa jama'ar garin Daura, mahaifarsa, baya bayan sun gamu da annobar ambaliyar ruwan sama.
A cikin makon jiya ne aka samu barkewar annobar ambaliyar ruwan sama a Daura sakamakon mamakon ruwan sama da ya zuba a garin.
A wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar, Buhari ya ce nan bada dadewa ba hukumar bayar da agajin gagga wa ta kasa (NEMA) zata sake sauke kayayyakin tallafin a garin Daura domin raba wa jama'ar da annobar ta shafa.
Jawabain ya kara da cewa, "sabanin zargin da ake yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan cewa ya juya wa jama'ar garin Daura baya, mu na masu tabbatar da cewa an raba wa jama'ar da annobar ta shafa kayan tallafi a cikin sa'a 48 da faruwar annobar ambaliyar ruwa. "Ya zuwa yanzu an raba wa jama'a kayan tallafi da aka kai a cikin tireloli goma. Daga cikin kayan tallafin da aka raba musu akwai kayan gini da suka hada da kwanon rufi, katako, siminti da kuma kayan abinci da sauran kayan tallafin gaggawa.
"Kazalika an raba musu barguna da katifu.
"An damka kayan ne a hannun masu ruwa da tsaki, kuma sun raba wa jama'a, don hatta sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, ya yaba wa hukumar NEMA bisa daukan mataki a kan lokaci."

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad